Isa ga babban shafi
Amurka

Ma'aikatun gwamnati za su iya kasancewa a rufe tsawon shekara 1

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya rufe wasu ma’aikatun gwamnatin kasar fiye da tsawon shekara daya matukar dai ya gaza samun kudaden da ya bukaci domin gina katanga tsakanin kasar da Mexico.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社。
Talla

Shugaba Trump ya furta wannan barazana ce, bayan da aka tashi baram-baram a jiya juma’a tsakaninsa da ‘yan jam’iyyar Democrat da ke da rinjaye a majalisar wakilan kasar, dangane da bukatar da ya gabatar ta samar da dala milyan dubu biyar domin fara aikin gina katangar.

An dai share tsawon makonni wasu ma'aikatun gwamnatin tarayya na rufe sakamakon rashin kudaden da za su tafiyar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.