rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Najeriya Ghana Saudiya Tarayyar Turai Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta kare Najeriya da Ghana wajen yaki da rashawa

media
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari Reuters/Carlos Barria

Kasar Amurka da Kungiyar da ke Yaki da Halarta Kudaden Haramun da ke Afrika ta Yamma, GIABA sun yi watsi da matakin Kungiyar Tarayyar Turai na sanya sunayen Najeriya da Ghana da Saudi Arabia cikin jerin kasashe 23 da ke nuna gazawa wajen yaki da halarta kudaden haramun a duniya.


Shugaban Kungiyar Yaki da Halarta Kudaden Haramun ta duniya, Billingslea Marshall ya bayyana rahotan Kungiyar Turai a matsayin mai cike da kura-kurai, yayin da Amurka ta bukaci watsi da rahotan saboda illar da zai haifar wajen kokarin da wadannan kasashe ke yi.

Kasashe irin su Japan da Argentina da wasu daga Afrika da Gabas ta Tsakiya duk sun goyi bayan Amurka kan wannan matsayi saboda abin da suka kira rashin bin hanyar da ta dace wajen nazarin matakan da kasashen ke dauka domin yaki da cin hanci da kuma halarta kudaden haramun.

Amurka ta ce, sake nazarin matakin da Najeriya ke dauka da kuma mayar da ita cikin kasashen da ke kungiyar ‘Egmont’ da ke tattara bayanan asiri domin yaki da halarta kudaden haramun, tabbaci ne kan yunkurin kasar na samun nasara.

Kwamishiniyar Shari’a ta kungiyar EU, Vera Jourova ta ce, sun sanya sunayen kasashe 23 cikin su har da Najeriya da Saudi Arabia ne sakamakon bayyanan da suka tattara, amma kuma rahotan nasu bai samu amincewar sauran mambobin kasashen Turai ba har sai an gudanar da wani taro nan gaba.