Isa ga babban shafi
NATO-Amurka

Kasashe mambobin NATO 7 sun kara kasafin tsaronsu bisa bukatar Amurka

Kasashen Kungiyar tsaro ta NATO 7 daga cikin mambobinta 29 sun bi sahun Amurka wajen bayar da kasafin kudin tafiyar da harkokin tsaron kungiyar yadda ake bukata, matakin da tuni Amurka wadda ta jima ta na fafutuka kan rashin cika kasafin ta yi maraba da shi.

Sakatare Janar na hukumar tsaron NATO Jens Stoltenberg
Sakatare Janar na hukumar tsaron NATO Jens Stoltenberg Reuters/路透社
Talla

Baya ga kasar ta Amurka kasashen kungiyar tsaron ta NATO da suka kunshi Birtaniya da Estonia da Girka da Latvia da kuma Lithuania da Poland sun amince da kashe kashi 2 na kasafin ga banagren tsaro.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya jima ya na fafutukar ganin ilahirin kasashen 27 sun yi amanna da matakin don karfafa kungiyar ta NATO.

Kasar Jamus, wadda ita ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar ta Turai ta na kashe akalla dala biliyan 45 ne a banagren tsaronta yayinda yanzu haka ta sanar da karawa zuwa dala biliyan 50 wanda ke matsayin kashi 1 da rabi sabanin kashi 2 da NATO ke bukata.

Tuni dai Sakatare Janar na kungiyar tsaron ta NATO, Jens Stoltenberg ya yi maraba da matakin sai dai ya ce akwai bukatar Jamus ta kara yawan kasafin don cimma muradan kungiyar nan da shekarar 2024.

Ko a watan Janairun da ya gabata ma, Stontelberg ya yi ikirarin cewa matsin lambar da kasashen ke fuskanta daga Amurka, ya sanya su amincewa da kara kasafin kudin na su ga bangaren tsaro, inda rahoton NATO na shekarar 2018 ke nuna cewa an samu karuwa sosai a banagren kasafin kungiyar.

Kafin yanzu dai Trump ya jima ya na zargin kasashen da dorawa Amurka nauyin tsaronsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.