rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Mozambique Zimbabwe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana fargabar mutuwar fiye da mutane dubu 1 a guguwar Mozambique

media
Guguwar wadda ta haifar da ambaliyar ruwa yanzu haka ta haddasa ambaliyar ruwa a birnin na Beini tare da lalata kashi 90 na gine-ginen birnin AMOS GUMULIRA / AFP

Fiye da mutane dubu guda yanzu haka ake fargabar sun rasa rayukansu, kari akan mutane 150 da aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu da dama da suka bace a kakkarfar guguwa mai dauke da ruwan sama da ta dirarwa kasashen Mozambique da Zimbabwe.


Kakkarfar guguwar wadda aka yiwa lakabi da Idai ta faro ne tun daga Alhamis din makon jiya a birnin Beira da ke tsakiyar Mozambique kafin daga bisani ta tsallaka kasar Zimbabwe.

Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya ce har zuwa safiyar yau adadin mutane 84 ne suka mutu amma zuwa tsakiyar ranar yau da abin ya tsananta, an akwai fargabar adadin wadanda suka mutu a Ibtila'in ya haura dubu 1.

Cikin sanarwar da shugaban ya fitar a yammacin yau Litinin ta ce fiye da mutane dubu dari yanzu haka na cikin hadarin rasa rayukansu a birnin na Beira mai yawan al'umma dubu dari biyar da 30.

Sanarwar ta ce kakkarfar guguwar wadda ta haddasa ambaliyar ruwa, yanzu haka ta rushe kashi 90 cikin 100 na gidajen birnin.