Isa ga babban shafi
Albania

Kakkarfar girgizar kasa ta afkawa Albania

Mahukunta a Albania sun tabbatar da mutuwar mutane 13 yayinda wasu 150 kuma suka jikkata sakamakon wata kakkarfar girgizar kasa mai maki 6.4 da ta afkawa Kasar da sanyin safiyar yau Talata.

Wani bangare da aka fuskanci girgizar kasa.
Wani bangare da aka fuskanci girgizar kasa. REUTERS/Beawiharta
Talla

Ma’aikatar tsaron albania da ta tabbatar da lamarin takuma bayyana yadda wani magidanci ya rasa ransa a kokarinsa na gujewa girgizar kasar inda ya fado daka kan wani dogon gini ya mutu.

Sanarawar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, anyi nasarar ciro gawarwakin dukkannin mutanen hudu ciki har da mace daga cikin baraguzan gine-gine.

Ma’aikatar lafiya ta Albania ta bayyana cewa mutane 150 yanzuhaka na fuskantar kulawar gaggawa a biranen Tirana da Durres da ke Arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.