Isa ga babban shafi
Kirismati

Dandazon jama'a na ziyara a mahaifar Yesu Al-Masihu

Masu ziyarar Ibada daga sassan duniya sun hallara a birnin Bethlehem mai tsarki da ke zama mahaifar Yesu Al-Masihu domin gudanar da bikin Kirismati na bana.

Dandazon jama'a sun hallara a birnin Bethlehem a jajibirin ranar Kirismati
Dandazon jama'a sun hallara a birnin Bethlehem a jajibirin ranar Kirismati REUTERS/Mussa Qawasma
Talla

Tun da sanyin safiyar wannan Talatar ce, Falasdinawa da baki daga kasashen waje, suka fara dandazo a wannan karamin birnin na Bethlehem da Isra’ila ta mamaye a yankin Yamma ga Kogin Jordan, yayin da ake gudanar da bukukuwa a ciki da wajen Majami’ar Nativity a wannan rana ta jajibirin Kirimati.

Masu yawon bude sun yi layi domin ziyartar kogon da ke cikin Majami’ar, inda aka yi amanna cewa, nan ne aka haifi Al-Masihu.

A cikin wani yanayi na sanyi da fitowar rana, daruruwan jama’a sun bai wa idanunsu abinci a daidai lokacin da ‘yan kungiyar agaji ta Boys Scout ke fareti da kide-kide na nishadantarwa.

Wata mata mai suna Germana da ta yi balaguro daga Italiya tare da mijinta da ‘ya’yanta ta ce, tana jin wani irin dadi na kasancewarta a wanann wuri a yau,

Ana sa ran Archbishop Pierbattista Pizzaballa, babban limamin Cocin Katolika a yankin gabas ta tsakiya, ya jagoranci taron addu’a na musamman a daren yau a can birnin na Bethlehem, yayin da ake kuma ake sa ran halartar shugaban Falasdinu Mahumud Abbas.

Birnin Bethlehem na kusa da birnin Kudus, amma Isra’ila ta yi amfani da katanga wajen raba shi da birnin na Kudus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.