Isa ga babban shafi
Sudan

An Rantsar Da Shugaba Omar al-Bashir

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ayau yayi alkawarin cigaba da harkoki da kasashen Turai, duk da cewa akwai umarni daga Kotun kasa da kasa, cewa a kamashi duk inda aka ganshi.Shugaban na magana ne bayan an rantsar dashi dazunnan, domin sabon waadin Shugabancin kasar na shekaru biyar.A watan jiya ne dai Omar al-Bashir ya lashe zaben da akayi, da jamiyu da yawa, bayan ya kwashe shekaru 21 yana mulkin kasar.Yayi alkawarin kaddamar da sabon yunkurin dinke duk wata baraka dake haifar da sabani a kasar, gabanin zaben raba gardama dake tafe watan Janairu na badi don neman ‘yancin kudancin kasar.Shugaba Omar al-Bashir yayi jawabin nasa ne ga wakilan majalisar kasar bayan rantsuwan kama aiki, inda wasu Shugabannin kasashen Africa shida suka halarta.Daga sauran kasashen duniya babu wakilai sosai.Shugaba Omar al-Bashir ya kasance Shugaba na farko da kotun kasa da kasa ta nemi a kama mata shi saboda laifukan yaki a yankin Darfur.A jiya wani na hannun daman Shugaban yace babu sauran batun sulhu da ‘yan tawayen yankin Darfur, musamman ‘yan kungiyar Justice and Equality Movement, JEM.   

shugaba Umar Hassan al Bashir
shugaba Umar Hassan al Bashir rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.