Isa ga babban shafi
Amurka-Gabar ta tsakiya

Kungiyar kasashen Larabawa sun amince da batun abkawa Syria

kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta gudanar da babban taron ta kan rikicin kasar Syria. Ana dai kallon taron a matsayin nuna mubayi’a ga kasar Amurka da kasashen Larabawan suka yi, Bayan da Amurkan ta bukaci kasashen Duniya da su amince da shirin ta na kai hari a kasar Siriya.  

Talla

Hitti Nassef shi ne mai Magana da yawun kungiyar kasashen Larabawa, ya kuma yiwa manema labarai bayani kan matakin da kasashen suka dauka kan kasar Siriya.
Gwamnatin kasar Iran dai ta yiwa daukacin kasashen Larabawan kashedi da cewar muddin suka amincewa Amurka kai hari a Siriya, to daukacin yankin na Larabawa zai shiga matsala don ba zura Ido kurum zata yi ba.

Masu lura da al’amurra dai na kallon Amurka a matsayin mai neman rafashewa wannan harin bayan da ta bayyana neman bukata daga Majalisar kasar.

Gwamnatin kasar Syria dai ta bukaci ‘yan Majalisar Amurka da suyi amfani da kaifin Basira domin nuna kin amincewqa da wannan mataki na Barack Obama, a yayinda ‘yan tawayen kasar Syria ke bukatar ‘yan Majalisa su amince..

Shugaba Bashar al-Asad dai ya yita nanatawa cewar ba zai yiyu ya yi amfani da Makami mai Guba ga ‘yan kasar sa ba, a yayin da suma dai kasashen Iran da Rasha basu goyi bayan kasashen Turai a kan sakamakon wannan bincike da aka gudanar ba, harma suna bayyana shi a matsayin makarkashiya.

Kasar Syria ta bayyana shugaba Barack Obama a matsayin wanda ya gigice, ya kuma rude saboda yanda ya zaburo da batun kai hari a Syria ya kuma rafashe.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.