Isa ga babban shafi
Isra'ila-Felesdinu

Kungiyar Kasashen Larabawa ta sauya matsayinta kan rikicin Isra’ila da Falasdinu

Kungiyar Kasashen Larabawa ta sauya matsayin ta kan shirin sasanta Isra’ila da Falasdinu, akan iyakokin ta na shekarar 1967, inda ta ce ta amince da wani sabon shiri da zai kaiga musayar wasu yankuna tsakanin bangarorin biyu. 

Kungiyar Kasashen Larabawa
Kungiyar Kasashen Larabawa www.intifada-palestine.com
Talla

Firaministan kasar Qatar, Hameed Jassin al Thani ya sanar da sabon matsayin cewar, bangarorin biyu na iya musayar wasu yankuna a tsakanin su, sabanin dagewar da suka yi a baya cewar, sai an baiwa Falasdinu yankunan ta na shekarar 1967, bayan wani taro da suka yi da mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden a Washington.

Al Thani ya jaddada cewar, duk da yake suna bukatar ganin Falasdinu ta samu kasa ta kanta akan iyakar ta na shekarar 1967, ana iya musayar wasu yankuna, idan bangarorin biyu sun amince.

Kungiyar ta ce, muddin aka cimma wannan bukata, kasashen Larabawa za su amince da kafuwar kasar Isra’ila.

Taron ya samu halartar wakilan kasahsen Bahrain, Masar, Jordan, Qatar da Lebanon.

Sauran sun hada da Saudi Arabia, kungiyar Falasdinu da kungiyar kasashen Larabawa.

Tuni Isra’ ila ta bayana farin cikin ta da sabon matsayin, ta hannun babar mai shiga tsakani kuma tsohuwar Firaminista, Tzipi Livni, wadda ta bayyana matsayin a matsayin babban cigaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.