Ana zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Guinea-Bissau
A yau lahadi al’ummar Guinea Bissau na gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu, inda Jose Mario Vaz da kuma Nuno Gomez Nabiam ke karawa da juna.
Wallafawa ranar:
An dai kafa rumfanan zaben har guda dubu 3 da 48 a sassa daban daban na kasar, domin bai wa mutane dubu 775 damar jefa kuri’unsu, a wannan kasa da ta yi kaurin suna wajen aiwatar da juye-juyen mulki wanda sau dama kan haddasa asarar rayukan jama’a.
Daya daga cikin ‘yan takarar wato Jose Mario wanda ya samu kashi 40 cikin dari a zagayen farko na zaben, ya zargi jami’an tsaro da tursasawa magoya bayansa, yayin da abokin hamayyasar Nuna Gomez Nabiam ya yi kira da a kwantar da hankula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu