Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsayin APC da PDP game da dage ranar zaben Najeriya

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya wato APC ta yi kakkausarar suka a game da matakin dage ranar gudanar da zaben shugabancin kasa da kuma na ‘yan Majalisun dokokin tarayya.  

Sabon katin dindin na hukumar Zabe a Najeriya
Sabon katin dindin na hukumar Zabe a Najeriya Channels tv
Talla

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai jim kadan bayan da shugaban hukumar zaben ya tabbatar da haka, shugaban jam’iyyar ta Apc John Odigie Oyegun ya matakin a matsayin koma baya ga dimokuradiyyar Najeriya, to sai dai jam’iyyar ta yi kir aga al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu, yana mai cewa an dage zaben ne amma ba ta yadda za a hana gudanar da shi a wani lokaci.

Ita kuwa jam’iyyar da ke mulkin kasar wato PDP ta yi lale marhabin ne da matakin jakuda ranar zaben da makwanni 6 kamar dai yadda shugaban hukumar zabe Farfesa Jega ya yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.