Isa ga babban shafi
AFDB

Akinwumi Adesina ya lashe zaben Bankin raya Afrika AFDB

Ministan noma na Najeriya Akinwumi Adesina ya lashe zaben Bankin Raya kasashen Afirka AFDB, Wanda aka gudanar a birnin Abijan na kasar Cote d’Ivoire. Inda zai maye gurbin Donard Kaberuka.A wani taro da masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da wannan banki suka gudanar a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.

Sabon shugaban bankin raya Afrika Adesina Akinwumi
Sabon shugaban bankin raya Afrika Adesina Akinwumi
Talla

An dai zabi Akinwumi Adesina ne bayan da aka je zabe har zuwa zagaye na 6, inda ya samu kuri’u kasha 58 cikin dari, yayin da Bedoumra Kordje dan kasar Chadi ya zo na biyu da kasha 31 cikin dari na kuri’un.

Adesina mai shekaru 55 a duniya, zai maye gurbin Donard Kaberuka dan kasar Rwanda wanda ya kawo karshen aikinsa bayan shafe sama da shekaru 10 a matsayin shugaba, kuma zai karbi ragamar tafiyar da wannan banki ne da ake kallo a matsayin daya daga cikin cibiyoyin kudade na duniya da ba sa fuskantar wata matsala a wannan zamani, duk kuwa da irin matslar tattalin arziki da duniya ke fama da ita.

Wakilai daga kasashe da kuma cibiyoyin da ke da hannun a Bankin Raya kasashen Afirka AFDB 80 ne suka gudanar da taro a birnin Abijan na kasar Cote d’Ivoire, cikin su akwai kasashen afrika 54 da wasu kasashen waje 26.

An dai haifi Adesina ne a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, kuma mahifinsa manoma ne, kuma ya samu digirinsa na farko ne a bangaren aikin gona a jami’ar Ife inda, kuma ya yi a kasar Amurka inda ya fito da digirin digirgir wato dakta.

Hakazalika ya yi aiki da kungiyoyi da dama na kasa da kasa kafin a nada shi ministan aikin gona a shekarar 2011. A yanzu kuma zai gaji Kaberuka  wanda a cikin shekarunsa 10 na shugabanci, ya taimaka matuka wajen ciyar da bankin gaba.

Wannan dai ya kasance lokaci na farko da Najeriya za ta shugabanci Bankin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.