Al-Bashir:Kotu ta yi watsi da bukatar gwamnatin Afrika ta Kudu
Babbar Kotun Afrika ta kudu ta ki amince wa da yunkurin gwamnatin Kasar na daukaka kara bayan an same ta da laifin kin kama shugaban Sudan Omar al-Bashir a lokacin da ya ziyarci Kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A ranar laraba ne babbar Kotun ta yi watsi da bukatar gwamnatin bayan an same ta da laifin barin al-Bashir har ya fice daga Kasar ba tare da tsare shi ba duk da cewa Kotu ta baiwa gwamantin umarnin cafke shi.
To sai dai gwamantin ta ce al-Bashir na da rigar kariya, abinda ya sa ta ki kama shugaban a lokacin da ya halarci taron Kungiyar Tarayyar kasashen Afrika.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC na neman al-Bashir ruwa a jallo sakamakon zargin sa da aikata laifukan yaki a rikicin yankin Darfur na Kasar Sudan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu