Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Ana wayar da kan masu zabe a Burkina Faso

A yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a Burkina Faso a ranar Lahadi mai zuwa, yanzu haka hukumar zaben kasar ta kafa kwamitocin tafi da gidanka domin kara wayar da kawunan al’umma dangane da inda za su gano rumfunansu na zabe.

A ranar 29 ga watan Nuwamba za a gudanar da zaben Shugaban kasa a Burkina Faso
A ranar 29 ga watan Nuwamba za a gudanar da zaben Shugaban kasa a Burkina Faso RFI/Olivier Rogez
Talla

A karkashin wadannan kwamitocin, jami’ai daga hukumar zaben ne ke zagayawa a cikin garuruwa, kauyuka da kuma kasuwanni domin sanar da jama’a muhimmanci fitowa zabe da kuma kaucewa karbar rashawa daga ‘yan siyasa.

Ana koyar da jama’a yadda za su yi amfani da wayar sadarwa domin gano inda ya kamata mutum ya jefa kuri’a.

‘Yan takara 14 ne zasu fafatawa a zaben, wanda shi ne karon farko bayan hambarar da Blaise Compaoré.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.