Isa ga babban shafi
Angola

Daurin shekaru 8 akan matasa 17 dake adawa da shugaba Dos Santos

Wata kotu a kasar Angola ta yankewa wasu matasa 17 daurin shekaru 2 zuwa 8 a gidan yari saboda samun su da laifin bore ga gwamnatin shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos.

Yan adawar kasar Angola
Yan adawar kasar Angola REUTERS/Herculano Corarado
Talla

Matasan ‘yan gwagwarmaya dai ana zarginsu ne da yunkurin juyin mulki da kuma ci gaba da yin adawa da mulkin shugaba Jose Eduardo Dos Santos, abinda yasa kotun yau litinin ta yanke hukuncin na zaman gidan yari na tsakanin shekaru 2 zuwa 8 akan su, kowanne bisa nauyin laifinsa

Alkalin ya kuma soma ne da Domingos Da Cruz wanda ya kira shugaban matasan kafin ya aiwatar da hukuncin zaman gidan yari na shekaru takwas da rabi akanshi

Sai kuma wani mawakin zamani da ake kira Luaty Beirao da ya sami shekaru 5 da watanni 6 bisa laifin yin anfani da takardun jabu wajen yarfa kalamun batanci akan shugaban kasar

Matasan dai basu nuna rashin da’a ba a tsawon lokacin da alkalin ya dauka wajen zartas da hukuncin har zuwa lokacin da aka wuce dasu gidan yarin.

Tun a watan yunin bara aka soma tuhumar Matasan da wadanan zarge zarge sai dai kuma sun musanta hakan inda suka bayyana kansu a matsayin matasan dake gwagwarmaya cikin lumana don tilastawa shugaba Dos Santos sauka daga mulkin kasar da ya kwashi tsawon shekaru 37 yana yi
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.