Isa ga babban shafi
Tanzania

Sojojin Tanzania sun yi wa mata Ciki a Congo

Majalisar Dinkin Duniya tace wasu ‘yan mata 11 daga Jamhuriyar Demokiradiyar Congo sun ce sojojin samar da zaman lafiya daga kasar Tanzania sun musu ciki. Kakakin Majalisar Farhan Haq yace 7 daga cikin matan har sun haihu, kuma 6 daga cikin su kananan yara ne.

Rundunar Sojin Monusco ta Majalisar Dinkin Duniya da ake aikin wanzar da zaman lafiya a Congo
Rundunar Sojin Monusco ta Majalisar Dinkin Duniya da ake aikin wanzar da zaman lafiya a Congo AFP PHOTO / ALAIN WANDIMOYI
Talla

Jakadan Tanzania a Majalisar Dinkin Duniay ya ce zasu tura tawagar masu bincike Congo don tabbatar da gaskiyar zargin.

Sojojin Tanzania dai na cikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da aka tura aikin wanzar da zaman lafiya a Mavivi lardin gabashin Arewavin Kivu mai fama da rikici a Jamhuriyyar Congo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.