Burkina ta soke sammacin kamo Guillaume Soro
Burkina Faso ta soke shelar kamo tsohon Firaministan kasar Cote d’Ivoire Guillaume Soro kan zargin da ake ma shi na hannu cikin yunkurin juyin mulkin da dakarun da ke biyayya ga tsohon shugaban kasa Blaise Compaore suka yi a kasar.
Wallafawa ranar:
Mai gabatar da kara a Burkina Alioune Zanre ne ya sanar da soke sammacin da kuma dorawa Cote d’Ivoire damar Soro wanda yanzu shi ne shugaban majalisa.
Dangantaka tsakanin Burkina Faso da Cote d’ivoire na ci gaba da tsami saboda yunkurin juyin mulkin.
Akalla mutane 11 suka mutu a yunkurin juyin mulkin wanda sojojin Burkina Faso suka murkushe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu