Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta ci zarafin mutane a yaki da Boko Haram- Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi Kamaru da keta hakkin mutane ta hanyar kame wadanda ake zargi suna da alaka da Boko Haram tare da azabtar da su.

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya AFP/Getty Images
Talla

Amnesty ta ce Kamaru na tsare da mutane sama da 1,000 a gidajen yarin da suka cunkushe wadanda aka kama kan zargin suna da alaka da Boko Haram.

Kuma ana tsare da mutanen ne ba tare kwararan hujjoji ba da ke tabbatar da suna da alaka da Boko Haram.

Sannan rashin ingancin gidajen yarin a Kamaru na sa mutanen mutuwa kusan a duk mako.

Amnesty ta ce mutane shida zuwa takwas ke mutuwa a wata a gidan yarin da ke garin Marwa.

Kungiyar ta ce tana da hujjoji akan mutane 29 da jami'an tsaron Kamaru suka azabtar tsakanin watan Nuwamban 2014 zuwa Oktoban 2015.

Sai dai gwamnatin Kamaru ta yi watsi da rahoton na Amnesty.

Mayakan Boko Haram dai sun kashe mutane da dama a Kamaru a hare haren kunar bakin wake da suke kai wa a yankin arewa mai nisa.

Sojojin Kamaru sama da 8,000 ne ke fada da Boko Haram da ke da'war jihadi a yammacin Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.