An kubutar da yara 145 daga hannu 'yan tawaye
Hukumar kula da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da nasarar kubutar da yara kanana 145 da ‘yan tawayen Sudan ta Kudu ke koyawa aikin soja.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa da ta fitar a birnin Nairobi na kasar Kenya, Hukumar ta bayyana cewa akwai yara kanana akalla dubu 16 da ke aikin sojan dole a kasar Sudan ta kudu, domin a bana kawai an dibi sama da 800 aikin sojan, har ma da bangaren sojin kasar.
A cewar Kungiyar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya an kubutar da yaran ne daga wata kungiyar mai sunan Cobra da kuma SPLA/10 dukkan su a gunduman Pibor.
Ko a bara a cewar sanarwar kananan yara 1775 aka kubutar daga aikin sojin.
Wadanan yara dai an kwace makaman da ke hannun su aka basu kayan sawa, kafin a yi masu huduba sosai a game da illar shigan su harkan soji da kananan shekaru.
Tun a shekara ta 2013 kasar Sudan ta kudu da ta ke murnar samun ‘yan ci daga Sudan ta fara yaki da ya hallaka mutane da dama wasu kuma aka tilasta masu yin hijira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu