Isa ga babban shafi
CAF

Aubameyang da Mahrez na takarar gwarzon Afrika

Dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang na cikin ‘yan wasa biyar da hukumar kwallon CAF ta ware domin zaben gwarzon dan wasan Afrika na bana.

CAF za ta zabi gwarzon Afrika tsakanin 'yan wasa biyar
CAF za ta zabi gwarzon Afrika tsakanin 'yan wasa biyar CAF
Talla

Sauran ‘Yan wasan sun hada da Riyad Mahrez da Islam Slimani ‘Yan kasar Algeria da ke taka kwallo a Leicester City ta Ingila. Da Sadio Mane na Senegal dan wasan kungiyar Liverpool da Mohamed Salah na Masar da ke wasa a kungiyar Roma ta Italiya.

Aubameyang ne ke rike da kambun kuma a bana ana ganin yana iya lashe kyautar. A bana Dan wasan ne na Gabon masanin raga ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Jamus.

Kodayake akwai Mahrez da ya taimakawa Leicester City lashe kofin Firimiya tare da jefa kwallaye 17 a raga a kakar da ta gabata.

A ranar 5 ga watan Janairu ne CAF zata zabi gwarzon dan wasan na Afrika a Abuja babbar birnin Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.