Za a dawo da mukamin Firaminista a Sudan
A yau Laraba majalisar dokokin Sudan ta kada kuri’a sake dawo da kujerar Firaminista bayan soke mukamin a shekara ta 1989 al’amarin da ya biyo bayan juyin mulkin da shugaba Omar al-Bashir ya jagoranta.
Wallafawa ranar:
Matakin dawo da kujerar Firaminista a kasar zai yi tasiri ga sauye-sauye da gwamnatin al-Bashir ke shirin aiwatar wa bayan cimma yarjejeniyar hadin kan kasa tsakanin gwamnatinsa da kungiyoyin ‘yan adawa.
Shugaba al-Bashir ya soke kujerar Firaministan ne bayan jagoranta juyin mulki da ya kifar da Gwamnatin Sadiq al-Mahdi da taimakon sirikinsa, Hassan al-Turabi jogoran muslunci na wanann lokaci a kasar.
A watan Oktober, bayan shafe sama da shekaru 25 kan karagar mulki, al-Bashir ya amince da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar da aka jimma ana zub da jini da kuma farfado da tatatlin arzikin kasar.
A ranar 10 a watan oktoba, shugaban ya gabatar sabon kudirin tsarin mulkin kasa, wanda ya samu amincewar ‘yan majalissu 387 daga cikin 425.
Sabon kudin tsarin mulkin a yanzu zai bai wa sabon Firaministan karfin ikon mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu