Al-Bashir ya ce sai Shekarar 2020 zai sauka daga Mulki
Shugaban Sudan Umar Hasan Albashir ya ce zai sauka daga mukaminsa amma sai a shekara ta 2020 idan Allah ya kai mu wanda shi ne karshen wa’adin mulkin da yake kai a yanzu.
Wallafawa ranar:
Albashir dai ya dare kan karagar mulkin kasar tun 1989 ta hanyar juyin mulki. Yanzu haka kotun duniya na nemansa domin hukunta shi a game da zargin aikata laifufukan yaki a yankin Darfur da cin zarafin bil’adama.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 300 aka kashe a yakin Sudan, kana sama da miliyan biyu da rabi sun kauracewa gidajensu saboda rashin kwanciyar hankali, alkallumar da ya zarce wanda Khartoum ta fitar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu