Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na shan suka kan hana baki shiga Amurka

Shugabanin Kasashen Duniya na ci gaba da sukar matsayin Donald Trump na hana baki Musulmi shiga Amurka dokar da tuni ta haifar da fito na fito a kasar.

Donald Trump ya ce yana kan bakarsa na hana baki shiga Amurka.
Donald Trump ya ce yana kan bakarsa na hana baki shiga Amurka. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shugabanin kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Iran da Indonesia duk sun bayyana matakin na Amurka a matsayin abinda ya sabawa dokokin duniya.

A wani taron shugabannin Yammacin Kasashen Turai da aka gudanar a karshen mako, shugaban Faransa Francois Hollande ya ce, ya zama dole su shirya tattauna da sabuwar gwamnatin Amurka, wadda ke nuna cewa, tana da nata tsarin wajen tinkarar matsalolin da dukkanin mu ke fuskanta.

Tsare-tsaren shugaban na Amurka Donald Trump na neman sukurkuta tsarin huldar da ke tsakanin Amurka da Turai, in da ya kira kungiyar tsaro ta NATO da tsohon yayi.

Dubban Amurkawa ne suka shiga wata zanga zanga a garuruwa daban daban na Amurka dan ci gaba da nuna adawar su da dokar hana baki Musulmi shiga kasar daga kasashe 7.

An kuma gudanar da irin wannan zanga zangar a tashoshin jiragen sama da ake tsare da baki maus zuwa kasar a biranen Los Angeles da Atalanta da Birnin Kansas da Baltimore da Denver da kuma Seattle.

A bangare guda, Donald Trump ya sanya hannu kan takardar umarni, don dakatar da bakin haure shiga Amurka, yayin da kuma ya sanya tsauraran matakai kan matafiya zuwa Amurka daga kasashen Musulmai guda bakwai.

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta caccaki matakin Trump na hana baki shiga kasarsa, in da ta ce, babu adalci wajen kuntata wa jama’a saboda banbancin addini.

Ita ma dai Firaminsitan Birtaniya Theresa May, ba ta amince da matakin Trump ba, sannan ta ce, za ta tsoma baki matukar hakan ya shafi al’ummar Birtaniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.