Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 100,000 Boko Haram ta kashe a Borno

Gwamnan Borno Kashim Shettima ya ce kimanin mutane 100,000 kungiyar Boko Haram ta kashe a jihar, sannan sama da mutane miliyan biyu ne rikicin kungiyar ya raba da gidajensu tare da janyo wa yankin hasarar kudi kimanin dala biliyan 9.

Tun 2009 Mayakan Boko Haram suka kaddamar da yaki a Najeriya
Tun 2009 Mayakan Boko Haram suka kaddamar da yaki a Najeriya Youtube
Talla

Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da ya ke jawabi game da rikicin Boko Haram a Jihar Borno a taron tunawa da tsohon shugaban Najeriya Janar Murtala Muhammad da aka gudanar a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja.

Gwamnan ya gabatar da takarda ne mai taken “Kula da rikicin Boko Haram, darasi ga Najeriya mai yawan kabilu da addinai da kuma Jam’iyyu”.

Takardar da gwamnan ya gabatar na kunshi ne da alkalumman girman hasarar da rikicin Boko Haram ya janyo wa jihar Borno tun soma rikicin har zuwa watan Disemban 2016.

Daga cikin mutane sama da miliyan biyu da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, gwamnan ya ce, sama da dubu dari biyar daga cikinsu sun warwatsu a sansanonin ‘Yan gudun hijira a cikin Maiduguri.

Sannan akwai wasu 379,614 a sansanonin ‘Yan gudun hijira a Bama da Banki da Pulka da Munguno da Ngala da Sabon Gari da Gwoza da kuma wasu wuraren a sassan Jihar Borno.

Gwamnan ya ce suna da alkalumman yawan marayu 52,311 da Mata 54,911 wadanda mazajensu suka mutu a sakamakon rikicin Boko Haram.

Kashim Shettima ya kuma bayyana takaicinsa akan yadda aka mayar da rikicin Boko Haram na kabilanci a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan musamman yadda wasu suka fito suna cewa shugabannin arewa ne suka kafa Boko Haram domin dagula gwamnatin Jonathan.

Ya ce ya yi mamakin yadda zargin ya yi tasiri ga Jonathan, inda ya bayar da misali cewa a lokacin da shugaban ya ziyarci Maiduguri a watan Maris na 2013, ya bukaci ya yi ganawa ta daban da shugabannin Kiristoci da kuma bangaren Jama’atul Nasril Islam ba tare da ya sanar da gwamnatin Borno ba.

Sai dai kuma a cewar gwamnan daga baya shugaba Goodluck Jonathan ya fahimci cewa mayakan Boko Haram sun fi kai wa musulmi hari fiye da kiristoci, bayan ya gana da bangarorin biyu.

Mista Shettima ya ce an siyasantar da rikicin Boko Haram a zamanin mulkin Jonathan da kuma Buhari. Musamman kan tsagerun Neja Delta da wasu ke zargin cewa suna kai hare hare ne domin dagula gwamnatin Buhari kamar yadda aka yi amfani da Boko Haram wajen dagula gwamnatin Jonatha.

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da banbancin kabila ko addini domin ci gaban kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.