Sule Lamido zai ci gaba da zama a gidan yari
Wata Kotu a Jigawa ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare tsohon gwamnan Jihar Sule Lamido a gidan yari har zuwa ranar 4 ga Mayu da za ta saurari bukatar bayar da shi beli kamar yadda lauyoyin da ke kare shi suka bukata.
Wallafawa ranar:
Kotun ta Majistire ta ce tana bukatar lokaci domin nazari kan karar da aka shigar gabanta kafin ta bayar da belin tsoho gwamnan.
Lauyoyin gwamnati ne suka yi watsi da bukatar bayar da belin Sule Lamido, lamarin da ya haifar da barkewar zanga-zanga daga bangaren magoya bayan tsohon gwamnan.
Ana tuhumar tsohon gwamnan na Jigawa da aikata laifuka guda hudu da suka shafi tayar da hankalin jama’a da rikici a jihar, zargin da Sule Lamido ya musanta.
A ranar Lahadi ne ‘Yan sanda suka cafke Sule Lamido a Kano tare da yin binciken kwa-kwaf a gidajensa da ke Kano da Jigawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu