Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Shekau ya musanta an raunata shi

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo yana musanta ikirarin sojojin Najeriya da suka ce ya ji mummunan rauni a hare haren sama da suka kai inda ya ke buya a cikin Jihar Borno.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau AFP Photo/Boko Haram
Talla

A makon jiya ne sojojin Najeriya suka ce hare haren jiragen sama da suka kai kauyen Balla kusa da dajin Sambisa ya kashe wasu shugabannin Boko Haram tare da raunana shugaban kungiyar.

Kodayake a sanarwar da ya fitar, Kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Usman Kukasheka bai ambaci sunan Shekau ba.

A cikin wani sakon bidiyo da aka wallafa a intanet, shugaban na Boko Haram ya yi watsi da ikirarin tare da cewa babu wani kwamandan shi da ya samu mummunan rauni.

“Ina nan a raye” inji Shekau.

Sannan a cikin bidiyon shugaban na Boko Haram ya yi nuni da yadda ya ke zaune a matsayin yana cikin koshin lafiya ba abin da ya same shi.

Amma kamfanin Dillacin labaran Faransa ya ruwaito wata majiya da ke da alaka da Boko Haram tana tabbatar da cewa Shekau ya ji rauni a harin da aka kai ta sama, inda sai da aka kwashe shi zuwa kusa da Kolofata kan iyaka da Kamaru.

Shekau ya sha fitowa yana karyata ikirarin an kashe shi ko an raunata shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.