Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Lauyan ‘yan awaren kamaru ya soki matakin Najeriya

Wani lauya a Najeriya ya ce matakin da kasar ta dauka na mika wa Kamaru shugabanni ‘yan aware da ake gani na mafaka a kasar ya sabawa dokoki.

'Yan sanda na kama masu zanga-zanga a yankin 'yan aware a Kamaru
'Yan sanda na kama masu zanga-zanga a yankin 'yan aware a Kamaru via REUTERS TV
Talla

Femi Falana da ke kare Shugabannin ya ce mika su bai dace ba la’akari da cewa al’amarinsu na gaban wata Kotun Tarayyar a Najeriya.

Mista Femi da ke bayyana Mutane a matsayin ‘yan gudun hijira ko masu neman mafaka ta siyasa ya ce babu wata hujja ko madogara na mika su ga gwamnatin Kamaru.

A cewar lauyan tun ranar da aka cafke shugabannin suka bukaci gwamnatin Najeriya ta sake su, idan kuma ba ta son zaman su a kasar to ta mika zancensu ga hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ke birnin Abuja.

‘A ranar Juma’ar makon da ya gabata shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya rubutawa gwamnatin Najeriya wasika kan matsayin wadannan mutanen karkashin tsarin dokar ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa, to amma sai gwamnatin ta yi kunnen-uwar-shegu, ta kori mutanen.’ A cewar Falana

Lauyan ya kuma ce bayan mutum 12, akwai wasu ‘yan kamaru 39 da aka kora daga Najeriya batun da ya ke cewa gwamnatin kasar ba za ta iya kare kanta ba a kan wannan abu da ta yi.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai na furgaban iya tuhumar wadannan mutanen kan laifin cin amanar kasa, wanda hukuncin wannan laifi a kamaru shi ne kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.