Benin
Yan Sanda sun capke wani dan Majalisa a Benin
A Jamhuriyar Benin an cakfe wani dan majalisar dokokin kasar Mohamed Atao, wanda ake zargi da dillancin kayayyakin da aka haramta shiga da su cikin kasar da suka hada da magunguna.
Wallafawa ranar:
Talla
A farkon shekarar 2018 ne yan sanda suka gano ta yadda ake shigowa da magunguna kasar ba bisa ka’ida ba,wanda bincike ya nuna cewa dan Majalisa Mohamed Atao na da masaniya a kai.
Tuni gwamnatin Patrice Talon ta gabatar wa majalisar dokokin kasar bukatar ganin an cire wa dan majalisar rigar kariya domin gurfanar da shi a gaban kotu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu