Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Ouattara bai yanke tsamanin sake tsayawa takara karo na uku ba

Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Dramane Ouattara ya ce bai kawar da yiyuwar sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku ba a shekara ta 2020 idan Allah ya kai mu.

Alassane Ouattara Shugaban kasar Cote D'Ivoire
Alassane Ouattara Shugaban kasar Cote D'Ivoire ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Ouattara wanda ke zantawa da mujallar Jeune Afrique, ya ce dalili na farko kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi a shekara ta 2016 ya ba shi wannan damar, to sai dai ya ce zai yanke hukunci ne a shekara ta 2020 lura da yanayi na zaman lafiyar kasar ko kuma akasin haka.

Ouattara mai shekaru 76 ya shaidawa Mujallar Jeune Afrique da ake wallafawa a Faransa cewar sabon kundin da za’a fara aiki da shi a 2020 ya baiwa kowa da kowa damar shiga zaben ba tare da sanya shinge ba.

A shekarar 2010 aka zabi Ouattara a wa’adin farko, zaben da ya haifar da tashin hankali lokacin da shugaba Laurent Gbagbo yace ba zai sauka daga kujerar sa ba, duk da kayen da ya sha, matakin da ya haifar da kashe dimbin rayuka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.