Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Jam'iyyar shugaba Kabila ta lashe zaben 'yan majalisu
Gamayyar jam’iyyun da ke kawance da shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila, sun lashe zaben ‘yan majalisun kasar da gagarumin rinjaye.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Sakamakon da hukumar zaben kasar CENI ta fitar a yau Asabar ya nuna cewa jam’iyyun kawancen na gwamnati sun lashe kujeru 280, daga cikin 429 da aka bayyana, yayinda ‘yan adawa suka samu kujeru 141.
Halin yanzu sakamakon zaben kujeru 71 ake ci gaba da dakon bayyanawa, a zaben majalisar Jamhuriyar Congon mai jimillar kujeru 500.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu