Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan Boko Haram sun sace mutane 13 a Diffa

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa wasu da ake zaton cewa magoya bayan kungiyar Boko Haram ne, sun yi awun gaba da mutane 13 a garin Tourmour da ke cikin jihar Diffa a yammacin jiya.

Sojin Nijar a sansanin 'yan gudun hijira na Boudouri a jihar Diffa, kudu maso gabashin Nijar
Sojin Nijar a sansanin 'yan gudun hijira na Boudouri a jihar Diffa, kudu maso gabashin Nijar REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shaidu sun ce maharan sun afka wa garin na Toumour ne dauke da makamai, inda suka yi awun gaba da wadannan mutane, yayin da shaidu suka tabbatar da cewa maza 10 da kuma mata uku ne aka maharan suka tafi da su.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da mayakan na Boko Haram ke yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa kafin su sake su a yankin na Diffa da ke daf da iyakar kasar ta Nijar da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.