Isa ga babban shafi

Musulmi suka fi jin radadin ta'addanci a duniya - Shugaban Nijar

Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issofou ya bayyana cewar kasha 82 na al’ummar duniya da hare haren ta’addanci ke ritsawa da su Musulmai ne, yayin da kasashen Musulmi ke kashe makudan kudade daga kasafin kudin su wajen yaki da ta’addanci.

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar mai ci.
Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar mai ci. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Yayin da yake bude taron kungiyar kasashen Musulmi ta duniya, wato OIC, karo na 47 a birnin Yammai, Issofou ya ce lokaci ya yi da kasashen Musulmi za su hada kan su, musamman wadanda ke Yankin Sahel wajen shawo kan matsalar ayyukan ta’addancin da ya addabe su.

Shugaban ya ce ya dace a dinga samu musayar bayanan asiri a bangaren soji da kuma aiki tare wajen shawo kan wannan matsalar da ta addabe su.

Issofou ya ce lokaci ya yi da shugabannin za su fahimci cewar yaki da talauci na daga cikin matakan yaki da ta’addanci da kuma tsatsauran ra’ayi, yayin da ya soki yadda 'yan ta’adda ke fakewa da addini suna aikata laifuffukan dake bata wa Musulunci suna.

Shugaban ya bukaci kungiyar OIC da ta mayar da hankali wajen aiwatar da manufofinta na shekarar 2025 wanda ke bukatar aiki tukuru wajen samun nasara.

Rahotanni sun ce ministocin kasashen waje daga kasashe 57 ke halartar taron, wanda zai mayar da hankali kan matsalolin da suka addabi duniyar Musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.