Isa ga babban shafi
Chadi-Deby

Ana gudanar da jana'izar Idris Deby a birnin N'Djamena na Chadi

Yau ake gudanar addu’o’i da kuma jana’izar tsohon shugaban kasar Chadi Chadi Idriss Deby Itno, wanda ya rasu  ranar litinin din da ta gabata a fagen daga, bayan raunin da ya samu a fafatawa da ‘yan tawayen kungiyar FACT kusa da garin Mao na lardin Kanem.

Gawar shugaban Chadi Idris Deby Itno.
Gawar shugaban Chadi Idris Deby Itno. © MARCO LONGARI/AFP
Talla

A jumlace shugabannin kasashe akalla 11 ne ake sa rai za su halarci jana’izar da suka hada da na kasashen yankin Sahel, sai kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda tuni ya isa a birnin Ndjamena.

Sai dai shugaban Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso ba zai samu damar halartar jana’izar ba saboda wasu dalilai, inda a maimakon haka kasar ta Congo za ta gudanar da makokin yini guda a  yau juma’a.

Majalisar Sojin kasar karkashin jagoranci Mahatma Deby ta sanar da daukar tsauraran matakan tsaro yayin jana’izar, yayinda jami’an tsaro na musamman ke ci gaba da sintiri a babban birnin kasar N’djamena da kewaye.

Shugabannin kasashen Afrika da suka isa kasar ta Chadi zuwa yanzu sun hada da  Alpha Conde na Guinea da shuagabn Mali Bah Ndaw sai Mahamat Ould Alghazwani na Murtania kana Mohamed Bazoum na Jamhuriyyar Nijar sai Umaro Embalo na Guinea Bissau sannan Firaminstan Gabon Madame Rose Oussouka.

Sauran shuwagabbanin kasashe da aka sanar za su halarci jana’izar sun kunshi Rock Kabore na Burkina Faso da Faure Gnassingbe na Togo kana Abdelfattah Al burhan na Sudan da kuma Felix Tshisekedi na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo .

Za a sallaci Idriss Deby a babban masallaci Malik Faysal bayan bikin na musamman kafin daga bisan a tafi da gawar zuwa garin Amdjaras a gabashin kasar don mikata ga iyalai da ‘yan uwan shugaban. 

Marigayi Idriss Deby Itno ya rasu ne a filin daga bayan raunukan da ya samu a fafatawa da ‘yan tawayen FACT a yankin Kanemi da ke da tazarar kilomita 300 daga birnin Ndjamena.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.