Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Mutane 117 sun mutu a rikicin Afirka ta Kudu

Kasar Afirka ta Kudu ta ninka yawan dakarunta a wuraren da rikici ya tsananta, a wani yunkuri na dakile ayyukan bata-gari da ke kokarin durkusar da tattalin arzikin kasar, yayin da alkaluman baya-bayan suka tabbatar da mutuwar mutane 117.

An kara yawan sojoji domin kwantar da tarzomar Afirka ta Kudu
An kara yawan sojoji domin kwantar da tarzomar Afirka ta Kudu REUTERS - SIPHIWE SIBEKO
Talla

Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar, ta ce zanga-zangar da ta sauya salo zuwa wawushe dukiyoyin jama’a tana bukatar daukar matakai, yayin da alkaluma na baya-bayan nan ke nuni da cewa an samu asarar rayukan mutane 117.

Gwamnatin kasar ta ce, an kara yawan dakaru dubu 25 domin daukar matakan gaggawa kan matsalolin da ke kokarin kawo tarnaki ga tattalin arzikin kasar, inda aka ninka yawan sojoji sau goman akan wadanda aka tura tun da fari.

Babban hafsan sojin kasar Laftanar-Janar Lawrence Mbatha ya ce an umarci sojoji su kawo karshen rikici da ke wakana, yayin da aka shiga kwana na shida da farawa.

Masu zanga-zanga sun lalata Manyan shaguna da rumbunan ajiyar kaya a lardunan biyu, wanda hakan ya haifar da nakasu ga hanyoyin samar da abinci, man fetur da magunguna, da tattalin arzikin masana’antun Afirka ta kudu ya dogara a kai.

A cewar alkalumman da aka fitar, mutane 72 sun mutu sannan an kame sama da mutane 1,200, yayin da hukumar kula da kayayyakin masarufi ta Afirka ta Kudu ta kiyasta cewa sama da shaguna 800 ne aka wawushewa dukiyoyinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.