Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu-Zuma

Rikicin Afirka ta Kudu ya haddasa karancin abinci

Biyo bayan lalata shaguna da sace-sacen da aka yi sakamakon rikicin da ya barke a Afrika ta Kudu, tun bayan da aka jefa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a kurkuku bisa laifin raina kotu, ana samun karancin  abinci da sauran kayayyakin masarufi a birnin Durban.

Jacob Zuma
Jacob Zuma Themba Hadebe POOL/AFP/File
Talla

A gaban wata cibiyar addinin Musulunci a birnin Durban motoci suka shiga layi don karbar burodi da madara. Al’ummar Musulmi ne suka bada gudummawar abinci  ba tare da wani sharadi ba.

Kimanin sunkin burodi dubu 60 ne ake rabawa duk rana, kamar yadda Abdul Razak Moosa, daya daga cikin jami’an dake rabon ya yi bayani.

Senzi Ndlovu  na daya cikin wadanda suka ci gajiyar wannan abin arziki, tafiyar minti 30 ta yi   a tasi don ta karbi nata rabon a cewarta.

Ba a sa ran  za a dade ana rabon abincin, amma kuma ana sa ran al’amura su koma daidai a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Yau ne Zuma ya bayyana a gaban kotu domin fara amsa tambayoyi game da zarge-zargen cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.