Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Sama da shuguna dubu 40 masu zanga zanga suka kona a Afirka ta Kudu

Mahukunta a Afirka ta Kudu sun ce sama da shaguna dubu 40 ne aka wawashe ko kuma aka kona a kwanakin da aka kwashe ana tarzoma a wasu yankunan kasar.

Wasu shaguna da zanga-zangar Afirka ya shafa a birin Alexandra na Johannesburg ranar 12 ga watan Yuli 2021.
Wasu shaguna da zanga-zangar Afirka ya shafa a birin Alexandra na Johannesburg ranar 12 ga watan Yuli 2021. AP - Yeshiel Panchia
Talla

Minista mai kula da kananan masana’antu a kasar Khumbudzo Ntshavheni, ta ce mafi yawan shagunan an kona su kurmus, yayin da wasu aka wawashe su, mafi yawa a lardin Kwazulu-Natal.

An lalala ofisoshin gidan waye da cibiyoyin raba kudade sama da 1,400 ciki har da bankuna 300, sai kuma gidajen sayar da magungunan 90.

Daga lardin Kwazulu-Natal ne tarzomar ta fara a  ranar  9 ga wannan wata na Yuli jim kadan bayan da aka sanar da cewa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya mika kansa ga jami’an gidan yari.

Daga bisani tarzomar ta kazance inda ta yadu zuwa Johannesburg tare da haddasa asarar rayukan mutane sama da 200, yayin da alkaluma ke nuni da cewa an wawashe dukiyar da ta kai ta euro bilyan 3 da milyan 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.