Isa ga babban shafi
AFIRKA-KORONA

Rikici ya barke akan raba maganin rigakafin korona

A kasar Afirka ta kudu, kungiyoyin dake yaki wajen ganin an raba maganin rigakafin cutar korona yadda kowanne sashe zai samu na hada kai sakamakon wani rahoton da Jaridar New York Times tayi, akan yadda akayi safarar allurar rigakafin Johnson and Johnson miliyan 32 da aka sarrafawa a kasar zuwa Turai.

Samfurin maganin Johnson & Johnson
Samfurin maganin Johnson & Johnson AP - Mary Altaffer
Talla

Kamfanin Johnson and Johnson yayi tsokacin cewar yayi iya bakin kokarin sa domin sanya Afirka ta kudu a gaba wajen samun maganin amma kuma rahotan yace an tirsasa masa ya sanya hannu akan wata yarjejeniyar yadda zai raba maganin da yake sarrafawa, abinda ya sa ake kwashe shi zuwa kasashen ketare.

Tuni wannan matsalar ta haifar da cece kuce a ciki da wajen kasar ta Afirka ta kudu.

Su dai wadannan magunguna da ake sarrafa su a Afirka ta kudu ana fita da su ne zuwa kasashen duniya, yayin da kasar ke fuskantar zagaye na 3 na annobar korona, abinda ya sa Fatima Hassan, mai kungiyar Justice Initiative tace ba zai yiwu ba.

Hassan tace Afirka ta kudu na matukar bukatar maganin rigakafin ciki harda wanda kamfanin Johnson and Johnson ke sarrafawa ganin yadda killace su ke da sauki, kuma hakan zai bada damar raba su ga yankunan karkara.

Afirka ta kudu na fatar yiwa kashi 70 na jama'ar kasar rigakafi nan da karshen shekara
Afirka ta kudu na fatar yiwa kashi 70 na jama'ar kasar rigakafi nan da karshen shekara Michele Spatari AFP

Yayin da kashi 2 bisa 100 ne kawai na mutanen Afirka suka karbi allurar rigakafin cutar korona, matakin ya zama abin takaici ga daukacin kasashen Afirka, kamar yadda Moses Mulumba, Daraktan Kula da lafiya da kare hakkin Bil Adama da kuma Cigaba na (CEHURD) a Uganda ya bayyana.

Moses yace wannan mataki da ‚yan mulkin mallaka ke amfani da Afirka wajen biyan bukatar kan su ba zai yiwu ba, yayin da a koda yaushe ake fada musu muhimmancin hada kai tsakanin kasashen duniya domin tinkarar matsalolin da ake samu.

Jami’in yace abin takaici ne daukar maganin baki daya ana kai su kasashen ketare yayin da Afirka ta kudu ke matukar bukatar su.

Ita kuwa Tlaleng Mofokeng, Mai binciken kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya cewa tayi kowa zai tafka asara muddin aka fifita jama’a wajen raba daidai na magungunan.

Mofokeng tace fifita wani sashe guda na duniya wajen bashi maganin rigakafin zai yiwa duniya illa domin kuwa matakin wata nasara ce na gajeren lokaci.

Jami’ar tace rowar maganin zai damar ci gaba da zama da cutar, kuma hakan na iya haifar da bore nan gaba.

Kungiyar Fatima Hassan tace a shirye take taje kotu idan an hana ta kwangilar raba magungunan nan da kwanaki masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.