Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Jami'ar 'yan sanda ta kashe 'yan uwanta na jini saboda kudi

Al’ummar Afrika ta Kudu sun cika da mamaki kan irin dabi’ar da wata jami’ar ‘yan sandan kasar ta nuna a daidai lokacin da Kotu ke yi mata shari’a kan zargin kashe ‘yan uwanta na jini domin handame kudadensu na inshora.

Jami'ar 'yan sandan Afrika da Kudu da ake zargi da kashe 'yan uwanta saboda da kudi.
Jami'ar 'yan sandan Afrika da Kudu da ake zargi da kashe 'yan uwanta saboda da kudi. © news24
Talla

Ana zargin Nomia Rosemary Ndlovu mai shekaru 46 da kashe ‘yan uwanta na jini su biyar da suka hada da saurayinta ta hanyar harbin su da bindiga da duka da guduma da kuma makure wuyansu har lahira.

Masu shigar da kara sun ce, jami’ar ‘yan sandan ta aikata kisan ne domin handame kudaden inshoran rai na mamatan da jumullarsu ya kai Dala dubu 93.

Wannan mummunan laifin da  aka ce Ndlovu ta aikata ya girgiza al’ummar Afrika ta Kudu, lura da cewa, suna yi mata kallon kwararriyar jami’ar tsaro mai gaskiya wadda kuma jama’a ke girmama ta a can baya.

Masu shigar da kara sun tattara hujjoji masu tayar da hankali  kan laifin da ake zargin ta da shi, yayin da a jiya Litinin ta  sake bayyana a gaban kotu domin ci gaba da amsa tambayoyi.

Sai dai wannan mata ta bai wa mutane mamaki, ganin yadda ta yi ta zunburo baki cikin girman-kai da kuma daga karan-hancinta a yayin zaman kotun.

Ndlovu ta isa harabar kotun cikin nuna kasaita, sanye da bakin takalmi mai tsini da kyalli da kuma koriyar taguwa, ga kuma wani dan gwado da ta yafa a kafadarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.