ANC na daf da samun sakamakon zabe mafi muni tun bayan zamanin wariya
Jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu na daf da samun sakamako mafi muni tun bayan mulkin wariya na apartheid, inda ake ganin goyon bayanta zai yi kasa da kaso 50 a zaben kananan hukumomi.
Wallafawa ranar:
A yayin da kaso 30 na rumfunan zabe suka sanar da sakamako biyo bayan zaben da aka gudanar a Litinin, Jam’iyyar African National Congress, ANC ta samu kaso 46 na kuri’un da aka kada, kamar yadda alkaluman hukumar zaben kasar suka nuna.
An yi yekuwa ga masu zabe da su fito su kada kuri’a zaben wadanda za su wakilce su a matakin kananan hukumomi da zumar kula da mahimman batutuwa da suka hada da wutar lantarki, samar da gidaje ruwan sha da tsaftar muhali.
Afrika ta Kudu ta shafe shekaru tana fuskantar ha’inci a game da yadda ake gudanar da al’amuranta, a yayin da jiga jigan jam’iyyar ANC mai mulki da suka hada da tsohon shugaba Jacob Zuma ke fuskantar tuhumar rashawa, kana rashin aikin yi ya kai sama da kaso 34 a kasar.
Har zuwa shekarar 2016, jam’iyyar ANC ce ta yi ta lashe kaso 60 na dukkannin kuri’un da ake kadawa tun da aka fara bai wa dukkan jinsina damar yin zabe a kasar, a a shakarar 1994, lokacin da aka rantsar da Nelson mandela a matsayin shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu