Jam'iyyar ANC ta Ramaphosa ta rasa rinjaye a zaben kasar
Jam’iyyar Shugaban kasar Afrika ta Kudu ta sha kayi a zaben wakilan hukumomin. Wannan dai ne karo na farko da jam’iyar marigayi Nelson Mandela ta fuskanci irin wannan kaye ,tareda samun kasar da kashi 50 cikin dari na sakamakon zaben da ya gudana.
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar ta rasa shida daga cikin manyan biranen takwas da ake da su a kasar.Wannan sakamakon zabe kan iya kai jam'iyyar ga rasa wasu daga cikin manyan kujeru tareda kai shugaban kasar Cyril Ramaphosa ga rasa kujerar sa a duk lokacin da ake zaben kasar.
Da samun wannan labari,kwamityn zartawa na jam’iyyar ANC ya kira taron gaggawa da wakilan jam'iyyar da nufin tattaunawa dangane da makomar jam’iyyar a wannan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu