Isa ga babban shafi
Gambia - Siyasa

Ana kidayar kuri'un zaben shugaban kasar Gambia

Jami’an zabe a Gambia na aikin tattara sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Asabar, wanda ke zama na farko da aka yi, tun bayan zaben da ya kawo karshen jagorancin tsohon shugaba Yahya Jammeh a shekara ta 2016.

Ma'aikatan zabe a kasar Gambia, a rumfunan kada kuri'u, yayin  tantance katunan shaidar zabe.
Ma'aikatan zabe a kasar Gambia, a rumfunan kada kuri'u, yayin tantance katunan shaidar zabe. © RFI/Laura-Angela Bagnetto
Talla

Jammeh wanda ya sha kaye a hannun kawancen 'yan adawa da suka marawa shugaba mai ci Adama Barrow baya, ya tsere zuwa Equatorial Guinea a shekarar 2017 bayan da ya ki amincewa da shan kaye.

‘Yan takara shida ne dai suka fafata a zaben shugabancin kasar Gambian da ya gudana a jiya, cikinsu har da shugaba mai ci Adama Barrow, da kuma babban abokin hamayyarsa Ousainou Darboe mai shekaru 73.

A Nuwamba, hukumar zaben kasar ta soke takarar mutane 15, yayin da ta amince da mutane shida da suka hada da shugaba mai ci Barrow, wadanda suka fafata a zaben da ya gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.