Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu ta yi rashin fitaccen mai yaki da wariyar launin fata

Shahararren limamin addinin Kirista da yayi fice wajen yaki da wariyar launin fata na Afirka ta Kudu, Archbishop Desmond Tutu, ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 90.

Desmond Tutu, fitaccen mai yaki da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.
Desmond Tutu, fitaccen mai yaki da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. AFP - RODGER BOSCH
Talla

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da mutuwar babban limamin cocin, inda ya bayyana jamamin rashinsa.

Ramaphosa ya bayyana mutuwar Archbishop Emeritus Desmond Tutu a matsayin wani babi na bakin ciki ga ‘yan Afirka ta Kudu da ma wajen kasar.

Kamafannin dillacin labarai na AFP ya bayyana cewa, dandazon masu makoki sun taru a wajen tsohuwar cocin marigayi Tutu ta St George's Cathedral, da ke birnin Cape Town, yayin da wasu suka yi cincirindo a gidansa rike da furannin furanni.

Desmond Tutu ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1984 saboda yaki da mulkin tsirarun fararen fata a kasarsa ta Afirka ta Kudu, zalika yayi fice wajen yaki da rashin adalci da kuma matsalolin da ke fuskantar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.