Guinea ta biya diyyar wadanda suka mutu saboda fashewar bama-bamai a 2021
Gwamnatin Equatorial Guinea ta biya diyya ga iyalai 84 na mutane fiye da 100 da suka mutu sakamakon fashewar bama-bamai a wani sansanin sojin kasar a shekarar bara.
Wallafawa ranar:
Fashe-fashen har kasha 4 sun auku ne a sansanin Nkoa Ntoma da ke birnin Bata, cibiyar tattalin arzikin kasar mai arzikin mai, inda mutane 107 suka mutu, yayin da wasu 615 suka jikkata a ranar 7 ga Maris na shekarar 2021.
Bayanai sun ce gwamnatin Equatorial Guinea ta ware CFA miliyan 700 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.1 ne don biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, inda iyalan wadanda suka mutu suka samu CFA miliyan takwas kowannensu yayin da wadanda suka jikkata suka samu CFA miliyan 4-4.
An yi taron mika diyyar ne a ranakun Juma’a da kuma Asabar karkashin jagorancin Teodoro Nguema Obiang Mangue, mataimakin shugaban kasa kuma dan shugaban kasar da ya dade yana mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu