Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Cin zarafin baki a Afrika ta Kudu tamkar mulkin wariya ne - Ramaphosa

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya caccaki jami’an sa-kai da suke cin zarafin bakin-haure a kasar, yana mai kwatanta dabi’arsu da irin tsarin ‘yan mulkin nuna wariyar launin fata.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa. REUTERS/Rodger Bosch
Talla

Mutane da dama sun yi ta gudanar da jerin zanga-zanga a ‘yan watannin nan domin nuna adawa da yawaitar kwararar bakin-haure a cikin kasar ta Afrika ta Kudu.

A makon jiya, an kashe wani mutun dan asalin Zimbabwe tare da kona gawarsa kurmus a garin Diepsloot da ke yankin arewacin birnin Johannesburg.

Wata tawagar jami’an sa-kai ta yi ta lekawa gida-gida tana bin diddigin asalin mutane bayan an kashe mutane bakwai a  garin na Diepsloot, yayin da wasu mazauna yankin suka soki ‘yan sanda kan yadda suka nade hannayensu ba tare da magance matsalar cin zarafin da ake yi wa bakin ba.

A wani sakonsa na mako-mako da aka wallafa, shugaban Afrika ta Kudun Cyril Ramaphosa ya ce, sun ga yadda wasu mutane fararen hula ke titse baki a kan tituna suna tilasta musu bayyana takardunsu  na shaidar izinin shiga cikin kasar .

Ramaphosa ya ce, irin wannan tsarin ne azzaluman da suka yi mulkin nuna wariya suka yi amfani da shi, inda a wancan zamanin ake kallon duk wani bakar fata tamkar mara gaskiya, sannan jami’an ‘yan sanda su ci zarafinsa musamman idan ya shiga yankin da fararen fata suka mamaye.

Shugaban ya kara da cewa, babu yadda za su bari irin wannan zaluncin ya  sake aukuwa a kasar ta Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.