Isa ga babban shafi

Qatar ta bukaci dage tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Chadi da 'yan adawa

Kasar Qatar wadda ke jagorantar shiga tsakani na tsawon makwanni shida tsakanin gwamnatin mulkin sojan Chadi da 'yan adawar kasar, ta bukaci da a dage cigaba da tattaunawar sulhun zuwa wani lokaci nan gaba.

Mahalarta taron tattaunawar neman zaman lafiyar kasar Chadi a birnin Doha na kasar Qatar. Ranar 13 ga Maris, 2022.
Mahalarta taron tattaunawar neman zaman lafiyar kasar Chadi a birnin Doha na kasar Qatar. Ranar 13 ga Maris, 2022. © AFPKARIM JAAFAR AFP/File
Talla

Sama da kungiyoyin 'yan adawa 40, da wakilan gwamnatin mulkin soja ne ke da tawaga a Doha tun ranar 13 ga Maris lokacin da aka bude tattaunawar farko a hukumance.

Shugaban mulkin sojan kasar ta Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, ya so a fara tattaunawar ta samar da zaman lafiya a Chadi, daga ranar 10 ga watan Mayu domin shirya zabe, amma har yanzu gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye, ba su gana ido da ido ba a tattaunawar da ya kamata ta zama ta sharar fage a Doha.

Sai dai a yayin da ‘yan adawa ke zargin gwamnatin Deby da yin kafar ungulu ga tattaunawar ta birnin Doha, gwamnatin Qatar ta ce shirin sasantawar da take jagoranta na samun ci gaba mai ma’ana.

Wannan ce ta sanya ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar yin kira ga kwamitin rikon kwarya na sojojin Chadi da ya dage babban taron tattaunawar na kasa, domin bayar da damar cimma wasu karin muhimman muradu.

Mahama Idris Deby, mai shekaru 38 a duniya, ya hau kan karagar mulkin Chadi ne kusan shekara guda da ta wuce, bayan mahaifinsa wanda ya dade yana shugabantar kasar Idriss Deby Itno, ya rasa ransa, bayan samun munanan raunuka a filin daga yayin fada da 'yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.