Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Chadi ta sake jinkirta tattaunawa da 'yan adawa

Gwamnatin mulkin sojan Chadi ta sanar da dage fara tattaunawar da za ta yi da dakarun 'yan tawaye da kuma 'yan adawa, a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen fara tattaunawa tsakanin bangarorin a Qatar.

Mahalarta taro yayin sauraren jawabin da ake fara ta attaunawar zaman lafiyar kasar Chadi a Doha babban birnin Qatar, a ranar 13 ga Maris, 2022.
Mahalarta taro yayin sauraren jawabin da ake fara ta attaunawar zaman lafiyar kasar Chadi a Doha babban birnin Qatar, a ranar 13 ga Maris, 2022. © AFPKARIM JAAFAR AFP/File
Talla

Gabanin tattaunawar da ake son farawa a ranar 10 ga wannan watan na Mayu, gwamnatin kasar da kuma kungiyoyin ‘yan adawa sama da 40 sun tura da wakilansu birnin Doha don share fage game da ganawar, duk da yake sun kwashe tsawon lokacin ba tare da sun gana ido da ido ba.

A lahadin nan da ta gabata ministan harkokin wajen kasar Chadi ya ce sun cimma matsayar sake dage taron, wanda tuni dama Qatar ta bukaci hakan.

A cewar Qatar hakan zai taimaka wajen samar da isasshen lokaci don cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

'Yan adawar dai na bukatar ganin Muhamat Deby bai shiga cikin harkokin zabe ba, da kuma baiwa ‘yan adawa tabbacin gudanar da zabe mai inganci.

Chadi dai ta shiga rudani ne tun bayan mutuwar shugaban kasar Idriss Deby Itno a watan Afrilun shekarar da ta gaba, lamarin da ya baiwa dansa Muhamat Idriss Deby damar ci gaba da jagorantar kasar da alkawarin gudanar da sahihin zabe a wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.