Isa ga babban shafi

Adadin wadanda ambaliyar ruwa ta kashe a Jamhuriyar Congo ya zarta 120

Sama da mutane 120 ne suka mutu a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, sakamakon ambaliyar ruwa mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru da dama bayan da ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin dare ya mamaye Kinshasa babban birnin kasar.

Wasu anguwannin birnin Kinshasa na jamhuriyar Congo da ruwa ta mamaye ranar 13 ga watan Disambar 2022.
Wasu anguwannin birnin Kinshasa na jamhuriyar Congo da ruwa ta mamaye ranar 13 ga watan Disambar 2022. AP - Samy Ntumba Shambuyi
Talla

Ruwa ta mamaya manyan tituna a tsakiyar birnin Kinshasa, mai kimanin mutane miliyan 15, na tsawon sa'o'i da dama, inda ta katse wata babbar hanyar samar da kayayyaki.

Adadinn farko

Adadinn farko dai mutane 55  hukumomi suka ce sun mutu ranar Talata, amnma ya zuwa wayewan laraba adadin ya haura 120.

Gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku daga ranar Laraba, a cewar wata sanarwa daga ofishin Firanminista Jean-Michel Sama Lukonde.

Shugaban ‘yan sandan kasar , Janar Sylvano Kasongo, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, akasarin mutanen da suka mutu sun kasance a gefen tuddai inda aka samu zaftarewar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.