Isa ga babban shafi

Mayakan sa kai suka kai wa sojojin Somalia hari duk da tsagaita bude wuta

A Somalia ‘yan ta’adda suka kaiwa wa sojojin kasar  hari a yankin Somaliland da ya balle, inda sojojin suka fatattaki ‘yan ta’adda, kamar yadda gidan talabijin din kasar ta Somaliland ya bayyana, duk da tsagaita bude wuta da mahukuntan kasar suka ayyana a yau asabar.

Wasu daga cikin mayaka da ke tafiya da kungiyar Al Shebab
Wasu daga cikin mayaka da ke tafiya da kungiyar Al Shebab ASSOCIATED PRESS - Mohamed Sheikh Nor
Talla

Rikicin ya barke ne a ranar Litinin din da ta gabata tsakanin dakarun sojin na Somaliland da kuma mayakan sa-kai masu biyayya ga gwamnatin tsakiyar Somaliya a garin las-anod da ke cikin jamhuriyar Somaliland mai cin gashin kanta.

Rikicin dai ya fara ne sa'o'i bayan da sarakunan gargajiya a yankin Sool, inda birnin Las-Anod, suka fitar da wata sanarwa da suka yi alkawarin goyon bayan "hadin kai da mutuncin Tarayyar Somalia", inda suka bukaci mahukuntan Somaliland da su janye sojojinsu daga yankin.

A safiyar yau asabar, ‘yan ta’addar sun kai wa rundunar sojin kasa ta Somaliland hari a birnin Las-anod, inda sojojin kasar suka yi nasarar murkushe su, kuma a halin yanzu suna cikin shirin ko-ta-kwana a sansanin sojinsu da ke Laas-Anod.

Abdiqani Mahamoud Ateye, Ministan tsaro na Somaliland, ya sanar da yammacin Juma'a da cimma batun "tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba".

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.