'Yan Malawi da guguwar Freddy ta daidaita na fuskantar barazanar yunwa
Mazauna karkara a Malawi na fuskantar barazanar yunwa da kuma wahalar balaguro sakamakon yadda guguwar Freddy, wadda ta taho da ruwan sama ta yi musu mummunan ta’adi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A farkon wannan makon ne, guguwar ta Freedy ta dirar wa kasar Malawi da ke yankin kudancin Afrika, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar laka wadda ta share gidaje da hanyoyi har ma da gadoji.
Masana yanayi sun ce, ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya cikin kwanaki shida a wannan kasa, daidai yake da ruwan sama na tsawon watanni shida.
Tuni wannan mamakon ruwan saman ya rarake tare da mamaye hanyoyi musamman a karkara, inda ala tilas mutane ke irin nasu dabaru wajen tsallaka ruwan domin balaguro
Wata mata mai juna biyu da mijinta sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP yadda ya zame musu dole su yi tafiyar kilomita 15 zuwa asibiti mafi kusa, duk da yadda ruwa ya mamaye hanya.
Wannan guguwar mai hade da ruwan sama ta yi sanadiyar mutwar mutane 438 tare da jikkata 918, sannan sama da dubu 345 sun rasa muhallansu kamar yadda alkaluman gwamnatin suka bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu