Isa ga babban shafi

An sake cafke wani fitaccen dan adawa a kasar Aljeriya

An kama dan adawar siyasar kasar Aljeriya kuma jigo a kungiyar masu rajin kare demokradiyya ta Hirak, Karim Tabbou, da yammacin ranar Talata a gidansa kuma aka tsare shi a hannun 'yan sanda, kamar yadda iyalansa da wasu kafafen yada labarai na cikin gida suka sanar.

Masu zanga-zanga dauke da tutar Aljeriya a ranar 9, ga Afrilu,2021.
Masu zanga-zanga dauke da tutar Aljeriya a ranar 9, ga Afrilu,2021. REUTERS - RAMZI BOUDINA
Talla

Tabbou ya kasance daya daga cikin fitattun mutanen da aka fi sani a yayin gangamin da ba a taba ganin irinsa ba, karkashin jagorancin kungiyar Hirak, wacce aka fara a watan Fabrairun 2019.

Magoya bayan sa dai sun bukaci a yi wa tsarin mulki garambawul tun bayan da kasar da ke arewacin Afirka ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekara ta 1962.

Tun a watan Maris din 2020 ne aka yanke wa Tabbou hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda laifin yiwa bangaren tsaro zagon kasa, sakamakon wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Facebook na jam’iyyarsa inda ya soki tsoma bakin sojoji a harkokin siyasa.

A shekarar da ta gabata ne aka saki Karim Tabbou bayan ya shafe shekara guda a gidan yari sakamakon yada kalaman batanci a shafukan sada zumunta a shekarar 2020 kan tasirin da sojoji ke da shi a siyasar kasar.

A cewar kwamitin 'yantar da fursunoni na kasar, mutane da dama da ke da alaka da 'yan kabilar Hirak ko kuma kare 'yancin kai na ci gaba da tsare a kasar Aljeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.